17 Satumba 2021 - 10:25
Shugaban Kasar Iran Ya Isa Dushambe Don Halattar Taron SCO

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra'isi ya isa birnin Dushambe babban birnin kasar Tajakistan don halattar taron SCO, inda ake saran Iran zata zama cikekken mamba a cikin kungiyar bayan sanya ido a cikinta na wasu shekaru. Shugaban kasar Tajakistan Emomali Rahmon ne gayyaci Ra'isi halattar taron sannan firai ministan kasar Kokhir Rasulzoda ya tarbeshi a tashar jiragen sama na Dushambe a safiyar yau Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Wannan dai shi ne tafiya ta zuwa kasashen waje ta farko tun bayan ya karbi shugabancin kasar Iran cikin farkon watan Augustan da ya gabata.

342/